IQNA

20:49 - November 19, 2018
Lambar Labari: 3483137
An gudanar da taron maulidin Manzon Allah (SAW) a cikin masallacin Quds mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da wani taron maulidin manzon Allah (SAW) a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

A yayin gudanar da zaman taron, Sheikh Sabri Ikrama babban malamin mai bayar da fatawa na Palastine ya bayyana cewa, taron maulidin manzon Allah (SAW) wata babbar dama ce ta fakar da al'ummar musulmi kan irin darussan da suke cikin rayuwa mai albarka ta manzon Allah.

Ya kara da cewa, halin da musulmi suka samu kansu a wannan zamani yana ban takaici, inda wasu daga cikin kasashen larabawa da na musulmi suka zama 'yan koren yahudawa masu kare siyasar yahudawa,a  daidai loacin da Isra'ila take tozarta addinin manzon Allah, take kashe musulmi a Palatine, take tozarta masallacin aqsa mai alfrma, alkiblar musulmi ta farko.

3764950

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: