IQNA

19:43 - November 30, 2018
Lambar Labari: 3483165
Taashar tralabijin ta CNN da ke kasar Amurka, ta kori dan rahotonta saboda nuna goyon baya ga al'ummar Palastine da kuma sukar lamirin Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Mark Lamant Hill dan rahoton tashar CNN ne, wanda ya yi jawabi a majalisar dinkin duniya, inda a cikin jawabinsa ya kirayi kasashen duniya da su haramta duk wani abu da yashafi Isra'ila.

Haka nan kuma ya jaddada kira ga kasashen duniya da su taimaki al'ummar Palastine domin samun 'yancin kansu daga kangin Isra'ila, wanda wannan furuci ya jawo masa kora a daga aikinsa.

Bayan korarsa, Marc Lamant Hill ya rubuta a shafinsa na twotter cewa, shi yana goyon bayan al'ummar Palastine, kuma yana sukar abin da Isra'ila take yi da kakausar murya na zaluntar al'ummar Palastine tare da tauye musu hakkokinsu a cikin kasarsu.

3768187

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Marc Lamant Hill ، Amurka ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: