IQNA

An Bukaci A Takawa Isra’ila Birki Kan Ginin Matsugunnai A Yankunan Palastine

23:54 - December 23, 2018
Lambar Labari: 3483244
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin wajen Palastine ta bukaci kasashen duniya da su taka wa Isra’ila birki kan wuce gona da iri da take yi a Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran SANA ya habarta cewa, ma’aikatar harkokin wajen Palastine ta bukaci kasashen duniya da su dakatar da Isra’ila kan ginin matsugunnan da take yi a  cikin yankunan Falastinawa.

Bayanin ya kara da cewa, dukkanin wuraren da Isra'ila take gina matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida, takan yi hakan ne da salo na musamman, ta yadda taswirar wuraren za ta kasance matsugunnan sun zagaye yankunan Flastinawa na asali da wuri, ta yadda za a wayi gari yankunan sun zama na yahudawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Palastine ta bayyana cewa, Isra'ila ta da wani shiri mai matukar hadari da take da niyyar aiwatarwa, wanda hakan ke nufin kawo karshen duk wani yunkurin zaman lafiya tsakaninta da Falastinawa.

Yanzu haka dai Isra'ila tana ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa da ke gabashin birnin Quds, bayan ta kammala mamaye dukkanin yankunan Falastinawa da ke yammacin birnin, kamar yadda take da shirin myar da dukkanin harkokin gudanarwa na gwamnati a birnin mai alfarma.

 

3775032

 

 

 

 

captcha