Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Becov ya fadi yau cewa, Rasha ta yi na'am da wannan mataki da rundunar sojin kasar Syria ta dauka, domin tabbatar da cewa ta dawo da ikon dukkanin yankunan kasar baki daya a karkashin gwamnatin kasar.
Ya ce wannan mataki zai taimaka matuka wajen gaggauta dawo da lamurra yadda suke a kasar Syria kafin barkewar rikicin da kasar ta yi fama da shi tsawon shekaru takwas a jere.
Kakakin fadar shugaban kasar rasha ya ce a halin yanzu kusan an riga an gama karya lagon 'yan ta'addan takfira kasar ta Syria, duk kuwa da irin mummunar barnar da suka yi kasar, da kuma kisan dubban daruruwan jama'a, amma hakan ya kawo karshe.
Bayan sanarwar da gwamnatin Amurka ta bayar kan janye sojojinta daga yankunan arewacin kasar Syria, inda take marawa mayakan kurdawa baya da suke rike da wasu garuruwa, a nata bangaren gwanatin Turkiya ta sanar da cewa za ta fara kaddamar da hari kan mayakan Kurdawan saboda suna a matsayin barazana a gare ta.
Wannan ya sanya a jiya Alhamis kurdawan suka nemi daukin dakarun Syria a jiya a garin Manbij, inda a yau sojojin Syria suka shiga cikin garin tare da daga tutocin kasar Syria a kowane sako na birnin, yayin da jama'ar garin suke ta murna na annawa kan hakan.