IQNA

Rikici A Kasar Sudan Na Ci Gaba Da Kara Kamari

20:06 - December 28, 2018
Lambar Labari: 3483260
Ministan watsa labaru na kasar Sudan ya yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa akan adadin wadanda jami'an tsaro su ka kashe a yayin Zanga-zanga.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kafar watsa labaru ta algad ta ambato ministan na watsa labari Bushara Jum'ah Arur yana cewa; Mutane sha tara ne kadai aka kashe, sai kuma dari hudu da shida da su ka jikkata

ministan watsa labarun na Sudan ya zargi masu Zanga-zangar da lalata dukiyar jama''a sannan kuma ya yi watsi da taken da suka riga bayarwa na sauya gwamnatin kasar.

Bushara ya ce; Batun sauya gwamnati yana da fuska ne ta doka, don haka ta hanyar zabe ne kawai za a iya samar da sauyi

Zanga-zangar Sudan ta shiga makwanni na biyu a jere, daruruwan mutane ne su ka fito kan tituna a cikin garuruwa da birane masu yawa na kasar domin nuna kin amincewa da karin farashin kayan masarufi.

Jami'an tsaron kasar sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu Zanga-zangar.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International' ta ce ya zuwa yanzu jami'an tsaron kasar ta Sudan sun kashe mutane sun kai talatin da takwas.

3776285

 

captcha