Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin Dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, a jiya sojojin Amurka sun harba bama-bamai masu haske da ake harbawa cikin samaniya domin haskaka wuri.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da sojojin Syria suka shiga cikin garin an manbij wanda yakea arewacin kasar Syria, inda kafin lokacin mayakan Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka ne suke iko da garin, inda bayan sanarwar da Amurka ta bayar kan fara janye dakarunta daga Syria, Kurdawan sun bukaci sojojin Syria su karbi iko da garin.
Kurdawan sun gabatar da wannan bukata ga sojojin Syria ne a ranar Laraba da ta gabata, da nufin takawa Turkiya birki a yunurinta na kaiwa Kurdawa haria yankin, inda a ranar Alhamis sojojin Syria suka shiga cikin birnin.
Sojin Amurka sun ce sun harba wadannan bama-bamai masu haske ne da nufin kaucewa taho mu gama tsakaninsyu da sojojin Syria, ta yadda za su iya ganin hanya da kuma wuraren da sojojin Syria suke domin kaucewa haduwa da su