IQNA

22:49 - January 04, 2019
Lambar Labari: 3483281
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar darul Quran a kasar Jamus ta yada wani faifan bidiyo na kira'ar Sayyid Mustafa Hussaini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin faifan tilawar Sayyid Mustafa Hussaini da aka yada a shafukan telegram, yana karanta surat Dariq.

Wannan makarancin kur'ani dan kasar Iran dai ya samu nasarar a lokacin gudanar da gasar kur'ani ta duniya karo na talatin da biyar, inda ya zoa  mataki na biyu a bangaren kira'a.

Sayyid Mustafa Hussaini da ne ga Azade wani wanda ya samu raunuka a wajen yaki dan garin Qazvin, ya tafi gasar kur'ani ta duniya a Kuwait tun yana da shekaru 18 da haihuwa, kuma ya zu matsayi na 3 a gasar.

Haka nan kuma a gasar kur'ani mai tsarki ta duniya da aka gudanar a kasar Malysia karo na 38, shi ne ya zo na hudu a gasar a bangaren kira'a.

3778120

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: