IQNA

Wata Tsohuwa ‘Yar Shekaru 75 Ta Hardace Kur’ani

23:56 - January 26, 2019
Lambar Labari: 3483330
Bangaren kasa da kasa Mansiyyah Bint Said Bin Zafir Al-ilyani wata tsohuwa ce ‘yar shekaru 75 da haihuwa a yankin Asir a kasar Saudiyya wadda ta hardace kur’ani baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wannan mata mai shekaru 75 da haihuwa ta fito n daga yankin Aljabila a cikin gundumar Asir a kasar Saudiyya, kuma ta fara hardar kur’ani ne tun shekaru 9 da suka gabata, inda ta fara da kananan surori.

Da farko dai ta fara yin amfani da na’urori na zamani domin yin harda, tana saurare kuma tana maimaitawa.

Haka nan kuma ta rika daukar sautin makaranta kur’ani tana binsu tana hardacwwa tana sake karantawa da kanta har wannn aya ta tsaya mata a cikin ka kafin ta ci gaba.

Mansiyyah ta ce tare da taimakon iyalanta da kuma karfin gwiwa da suke bata, ta samu damar ci gaba da yin wannan harda tsawon shekaru tara, inda a halin yanzu da yardarm Allah ta kammala hardar kur’ani baki dayansa.

3784331

 

 

 

 

 

 

captcha