IQNA

An Bukaci Da A Ware Wurare Domin Karatun Kur’ani Ga Masu Larori A Aljeriya

1:44 - January 28, 2019
Lambar Labari: 3483334
Bangaren kasa da kasa, an kirayi mahukunta a kasa Aljeriya da s ware wurare na musamman domin karatun kur’ani ga masu larura ta musamman.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Farida Jabali mataimakiyar shuagaban majalisar shawara ta birnin Aljier a kasar Aljeriya, ta bukaci mahukunta a kasa Aljeriya da s ware wurare na musamman domin karatun kur’ani ga masu larura ta musamman domin su samu damar gudanar da harkokinsu awannan fage cikin natsuwa.

Farida Jabali ta ce, akwai masu larura ta musamman da suke da hazka matuka a bangarori daban-daban musamman a bangaren kur’ani, inda ta ce maimakon barin masu son karatun kur’ani daga cikinsu haka nan, tana da kyau a ware musu wuri na musamman domin kula da su da karfafa musu gwiwa  akan hakan.

Ta ci gaba da cewa, babban abin da ae bukata a irin wadannan wurare shi ne malamai masu kwarewa wajen koyar da masu larura ta musamman, da kuma kayan aiki na zamani wadanda za su debe musu kewa, kuma su sanya su nishadi.

Haka nan kuma ta bayyana hakan a matsayin aiki mai kyau wanda yake tattare da lada ga wanda ya taimaka wajen aiwatar da shi.

3784942

 

 

 

captcha