IQNA

14:37 - February 04, 2019
Lambar Labari: 3483344
Bangaren kasa da kasa, Jagoran darikar 'yan katolika, Paparoma Francis, zai fara wata ziyara yau Lahadi a Hadaddiyar Daular Larabawa, wacce ita ce irinta ta farko ta wani Paparoma.

Kamfanin dillncin labaran iqna, Bayan irin wannan ziyara da ya kai a shekara 2014 a Turkiyya, sannan a Masar a shekaru biyu da suka gabata, Fafaroma Francis zai fara ziyara ta kwanaki a hadaddiyar daular larabawa, nada nufin kirabn hadin kan addinai akan zaman tare.  

Baya ga Hadaddiyar Daular Larabawa Fafaroma zai kai irin wannan ziyara a kasar Morocco a cikin watan Maris mai zuwa.

Hadadiyar Daular Larabwa dai na kunshe da mabiya addinin krista kashi 10% wadanda galibinsu 'yan rani ne dake aiki a kasar wadanda suka fito daga kasashen Indiya da kuma Philippines.

Yarima mai jiran gado na Hadaddiyar Daular Larabawan ne, Shaikh Mohammed ben Zayed al-Nahyane, da kuma karamar cocin katolika ta birnin Abou Dhabi suka gayyaci Paparoman.

A yayin ziyarar an tsara Paparoman  zai gana da manyan malaman addinin Islama, da na Buda, da yahudawa da kuma Hindu, da kuma yarima mai jiran gado na kasar, duka a yunkurin samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.

3787362

 

استقبال رسمی از پاپ فرانسیس در کاخ ریاستی ابوظبی

استقبال رسمی از پاپ فرانسیس در کاخ ریاستی ابوظبی

استقبال رسمی از پاپ فرانسیس در کاخ ریاستی ابوظبی

استقبال رسمی از پاپ فرنسیس در قصر ابوظبی

استقبال رسمی از پاپ فرنسیس در قصر ابوظبی

استقبال رسمی از پاپ فرنسیس در قصر ابوظبی

استقبال رسمی از پاپ فرنسیس در قصر ابوظبی

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، pop ، Abu Dhabi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: