IQNA

22:51 - February 09, 2019
Lambar Labari: 3483358
Bangaren siyasa, an gudanar da zaman makokin shahadar Sayyidah Fatima Zahra (AS) tare da halartar jagoran juyin juya hali.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yau an gudanar da zaman makokin shahadar Sayyidah Fatima Zahra (AS) tare da halartar jagoran juyin juya hali a Husainiyyar Imam Khomenei (RA).

A ayyin taron an gabatar da jawabai da suka shafi matsayinta madukaki, da kuma irin darussan da suke a cikin rayuwarta mai albarka, kamar yadda kuma aka yi makoki.

A kowace shekara kamar yadda aka saba akan gayyaci malamai dam asana da kuma jami’an gwamnati a wurin taron, inda kuma dubban mutane daga sassa daban-daban sukan halarci wannan taro mai albarka.

Sayyid Zahra (AS) diyar manzon Allah (SAW) ce wadda ta kasance mafi soyuwa  a gare shi a cikin rayuwarsa,kamar yadda kuma ya bayyana ta a matsayin tsoka ce daga cikin jikinsa mai albarka.

3788827

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، wadda ، matsayin ، jikinsa ، Zahra
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: