IQNA

Taron Mata Mahardata Kur’ani A Birnin Karbala Na Iraki

21:51 - February 10, 2019
Lambar Labari: 3483361
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron mata mahardata kur’ani mai tsarki karkashin kulawar cibiyar kur’ani ta Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka kamala taron mata mahardata kur’ani mai tsarki karkashin kulawar cibiyar kur’ani ta Karbala mai alfarma.

Taron wanda ya hada mata mahardata daga sassa na kasar Iraki shi ne irinsa na farko da aka fara gudanarwa, domin karfafa gwiwar sauran mata a kan lamarin kur’ani mai tsarki.

Mata mahardata kur’ani fiye da 250 ne suka halarci wurin taron, inda aka gabatar da jawabai da kuma wasu shirye-shirye na musamman na tsawon kwanaki uku a jere.

Baya ga haka kuma an bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka halrci taron,an kuma karrama su albarkacin alkur’ani mai tsarki.

3788875

 

 

 

captcha