IQNA

21:53 - February 10, 2019
Lambar Labari: 3483362
Bagaren kasa da kasa, an raba taimakon kayayyakin abinci wanda ya kai tan 100 ga al’ummar kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran UNA ya bayar da rahoton cewa hukumar bayar da agajin gaagwa ta kasar Kuwait Helal Ahmar ta raba taimakon kayayyakin abinci wanda ya kai tan 100 ga al’ummar kasar Yemen a wasu yankunan kasar.

Wannan taimako dai an raba shi a yankunan Ma’arib, Jauf, Aden da Hadra Maut, haka nan kuma mutane dubu 41 ne suka samu taimakon.

Tun bayan da masarautar al saud ta fara kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemena  fiye da shekaru uku da suka gabata, ya zuwa yanzu dubban fararen hula ne suka rasa rayukansu sakamaon hakan.

Kasashen turai ne dai suke sayar da makamai na biliyoyin dalli da msarauyatr domin ci gaba da kai wadannan hare-hare, da nufin rusa kasar musulmi da kuma kasashe dadai mai yawa na musulmi amma ta hanyarsu ba kai tsaye.

3788629

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، tan ، yemen ، kuwait
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: