IQNA

23:06 - February 12, 2019
Lambar Labari: 3483367
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani aiki na gyaran kwafin kur’anai a kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shadin gulf365.com ya bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da wani gagarumin aiki na gyaran kwafin kur’anai a kasar Sudan.

Bayanin ya ce wannan wannan aiki wata cibiya mai suna Dar Masahif Afrika ta fara gudanar da wannan aiki a fadin kasar.

Shirin dai zai hada da kur’anai da ake ajiyewa  acikin masallatai da makarantun addini da kuma cibiyoyin ilimi da dakunan kartu, kamar yadda kuma mutane da suke ajiye da daddun kur’anai a cikin gidajensu za su iya kawo kur’anan nasu a wannan cibiya domin gyaransu.

Muhammad Abdulkadir shi ne babban daraktan wannan cibiya, ya bayyana cewa an fara gudanar da wannan aiki cikin nasara, inda ya zuwa yanzu a cikin kwanaki biyu da fara aikinsu an gyara kur’anai da dama.

3789259

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: