IQNA

23:25 - February 13, 2019
Lambar Labari: 3483370

An Kashe Mayakn Kungiyar Al-shabab 12 A Cikin Kasar Somalia

Bangaren kasa da kasa, akalla mayakan kungiyar alshabab 12 ne Amurka ta ce ta kasha a cikin kasar Somalia a jiya.

An Kashe Mayakn Kungiyar Al-shabab 12 A Cikin Kasar Somalia

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Russia today ta bayar da rahoton cewa, dakarun Amurka da ke gabashin nahiyar Afrika sun ce sun kasha mayakan kungiyar Alshabab a cikin kasar Somalia ta hanyar yin amfani da jiragen yaki marassa matuki.

Sojojin na Amurka sun bayyana hare-haren nasu a cikin Somalia da cewa sun gudana cikin nasara, domin kuwa sun rage karfin ‘yan ta’adda.

Tun a cikin shekara ta 2011 ce dai dakarun kasa da kasa suka fara gudanar da ayyukan soji a cikin kasar Somalia da nufin murkushe kungiyar Alshbab wadda take da dangantaka da kungiyar Alkaida.

Amurka tana yin amfani da wannan damar domin kaddamar da hare-hare a cikin kasar Somalia da sunan taimakawa wajen murkushe kungiyar Alshabab.

3789994

 

 

 

 

captcha