IQNA

23:32 - February 13, 2019
Lambar Labari: 3483372
Bangaren kasa da kasa, majiyoyin tsaro a kasar Masar sun sanar da cewa an zartar da hukuncin kisa  a kan wasu mambobi 3 a kungiyar Ikhwan Muslimin a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Russia today ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin tsaro a kasar Masar sun sanar da cewa a jiya an zartar da hukuncin kisa  a kan wasu mambobi a kungiyar Ikhwan Muslimin a Masar su uku, bisa laifin kisan Nabil Faraj, wani babban jami’in ‘yan sanda na kasar Masar.

Tun shekaru 5 da suka gabata ne dai aka kasha Nabil Faraj a yankin Kardasa bayan kai wani hari.

Jami’an tsaron Masar 13 ne aka kasha a harina  cikin watan Agustan 2013, inda wasu mutane dauke da manyan bindigogi suka kaddamar da hare-hare a kan cibiyoyin tsaro, inda ake tuhumar wadannan mutane 3 da cewa suna daga cikin wadanda suka kaddamar da harin, kuma an zartar da hukuncin kisa  akansu.

3789993

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، masar ، zartar ، ikhwan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: