IQNA

22:58 - February 17, 2019
Lambar Labari: 3483380
Bangaren kasa da kasa, an shiga mataki na karshe na gasar cibiyar Azhar a lardin Aqsas na kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau an shiga mataki na karshe na gasar hardar kur’ani mai tsarki karkashin cibiyar Azhar a lardin Aqsas na kasar Masar.

Sheikh Abdulhalim Muhammad shugaban bangaren cibiyar Azhar a yankin Aqsar ya bayyana cewa, wannan gasa ta shafi daliban kur’ani ne kawai, kuma adadin wadanda suke cikin gasar ya kai dalibai 2775.

Ya ci gaba da cewa gasar tana gudana ne a dukkanin bangarori da ake gudanar da gasa, a mataki na farko da na biyu da kuma na uku.

Daga karshe cibiyar Azhar ta ware kyatuka masu tsoka ga dukkanin wadanda suka nuna kwazo a wannan gasa, inda za a bayar da kyautukan ga wadanda suka zo na daya da na biyu da kuma na uku.

3790702

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، azhar ، Aqsar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: