IQNA

23:44 - February 19, 2019
Lambar Labari: 3483384
Bangaren kasa da kasa, janar Pakpour ya bayyana cewa wadanda suka kai harin garin Zahedan na kasar Iran ‘yan kasar Pakistan ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Itan (IRGC), ta sanar da cewa wani dan asalin kasar Pakistan ne ya kai harin ta'addancin da ya yi sanadin shahadar mambobinta 27 a makon da ya gabata a yankin Sistan Balouchistan a kudu maso gabashin kasar.

Da yake sanar da hakan a wajen taron juyayi na rasuwar sojojin a nan birnin Tehran, kwamandan rundinar sojin kasa ta (IRGC), Janar Mohammad Pakpour, ya ce an tantance maharin, wanda sunansa, Hafez Mohammad-Ali, da ya fito daga aksar Pakistan.

Janar Pakpour, ya kara da cewa, zurfafa binciken da akayi kan motar da aka kai harin da ita shake da bama-bamai ne ya bada damar tantance maharin, da kuma wadanda suka taimaka wa maharin.

Dama kafin hakan, rundinar ta sanar da cafke mutum uku da ake zargi da hannu wajen shirya harin, da suka hada da 'yan Pakistan biyu ciki harda maharin.

Binciken da akayi ya gano cewa maharan sun shirya kai harin ne a ranar bikin cika shekaru 40 da nasara juyin juyin halin musulinci na kasar ta Iran da ya gudana a ranar 11 ga watan Fabrairun nan.

Harin da aka kai a ranar 13 ga watan nan, a yankin Sistan-Baluchistan dake kudu maso gabashin kasar ta Iran, a iyaka da kasar Pakistan, na daya daga cikin munannen hare haren da aka kai kan rundinar ta kare juyin juya halin musulinci na Iran.

3791619

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، Zahedan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: