IQNA

23:52 - February 19, 2019
Lambar Labari: 3483387
Bangaren kasa da kasa, an girmama yara mahardata kur’ani mai tsarki a yankin Sinai na Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Abu Dhabi ya bayar da rahoton cewa, an girmama yara mahardata kur’ani mai tsarki a yankin Sinai na Masar kuma dukkaninsu sun halarci gasar kur’ani ta makarantar Sheikh Abdulwahid tswon shekaru shida a jere.

An dai gudanar da zaman taron girmama wadannan yara ne a masalalcin Almanshiyya da ke yankin na Sinai.

Baya ga haka kuma an bayar da shedar girmamawa ta musamman ga kowane daya daga cikin yara, sakamakon kwazon da suka nuna kan sha’anin kur’ani mai tsarki.

3791736

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sinai ، Masar ، mahardata
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: