IQNA

22:14 - February 20, 2019
Lambar Labari: 3483390
Bangaren kasa da kasa, ministan Palestine mai kula da harkokin Quds ya bayyana cewa Isra’ila na rarraba masallacin Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Adnan Husaini ministan Palestine mai kula da harkokin Quds ya bayyana cewa Isra’ila na rarraba masallacin Aqsa zuwa bangarori daban-daban.

Ministan ya ce irin matakan da Isra’ila take dauka a halin yanzu a kan masallacin qasa na nuni da irin shirin da take da shi ne na rarraba wannan masallaci.

Ya ce masallacin Aqsa wakkafi na musulmi da babu yadda za a yi a raba shi, kuma daukar duk wani mataki makamancin wannan ba a bu ne da dukkanin musulmi na duniya za su amince da shi ba.

A jiya ne sojojin Isra’ila suka kaddamar da farmaki a kan masallacin Aqsa tare da rufe kofar babau rahma, wadda it ace kofar da muuslmi suke shiga cikin masallaci, inda suka jikkata musulmi da dama tare da kame wasu.

3791995

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، aqsa ، jikkata ، masallacin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: