IQNA

23:08 - February 21, 2019
Lambar Labari: 3483391
Bangaren kasa da kasa, Charles Awani wani malamin addinin kirista ne da ya musulunta kuma ya gina masallaci a inda majami’arsa take.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Mustafa Sawaki dya ne daga cikin malaman addinin musuluncia  garin Kisi, kuma Charles ya musulunta a hannunsa ta hanyar yin furuci da kalamar shahada da kadaicin Allah madaukakin sarki da kuma imani da manzzancin manzon tsira Muhammad (SAW).

Bayan musuluntarsa, kimanin mutane 65 daga cikin mabiyansa sun yi Kalmar shahada, inda suma suka karbi addinin musulunci tare dashi.

Yanzu haka an gina masallaci a wurin da  lokacin baya yake da wata majami’a, inda yanzu ake yin salla a wurin.

Haka nan kuma wannan malamin addinin kirista da ya karbi addinin muslucni ya bukaci da  a sanya masa suna Isma’il a matsayin sabon sunansa na musulunci.

Isma’ila Akwani ya bayyana cewa ya yi tafiye-tafiye a ciki da wajen kasar ta Kenya da kuma Tanzani, domin isar da sakon addinin kirista, inda a  halin yanzu kuma yana son ya ci gaba da aikinsa  amma a matsayin mai isar da sakon addinin muslunci.

3792172

کشیش کنیایی چگونه مسلمان شد؟+عکس

کشیش کنیایی چگونه مسلمان شد؟+عکس

کشیش کنیایی چگونه مسلمان شد؟+عکس

کشیش کنیایی چگونه مسلمان شد؟+عکس

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: