IQNA

23:10 - February 21, 2019
Lambar Labari: 3483392
Bangaren kasa da kasa, shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya kirayi dukkanin Falastinawa da su a birnin Quds daga zuwa ranar Juma’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna, hugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya kirayi dukkanin Falastinawa da su a birnin Quds daga zuwa ranar Juma’a domin takawa Isra’ila burki a yunkurinta na rarraba masallacin Aqsa.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a cikin sakon nasa, Haniyya ya bayyana cewa Isra’ila tana da nufin ganin bayan masallacin quds wanda yake a matsayin wakafi na dukkanin musulmin duniya.

Tun a ranar Litinin da ta gabata ce Isra’ila ta kwace iko da kofar Babu Rahma, kofar da musulmi suke shiga cikin masallacin aqsa.

A nasa bangaren ministan Palstinu mai kula da harkokin da suka shafi Quds ya bayyana cewa, manufar Isra’ila ita ce kakkabe hannun musulmi baki daya daga duk wani abin da ya shafi masalalcin Aqsa, tare da rarraba shi yadda ta ga dama.

3792059

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: