Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto majiyar Palasdinawa na cewa; A jiya Asabar, sojojin Sahayoniya sun kai hare-hare a yankuna daban-daban na yammacin kogin Jordan, tare da kame Palasdinawa masu yawa.
Majiyar Palasdinawa ta kara da cewa a wasu yankunan da ‘yan sahayoniyar suka kai hari, an yi taho-mu-gama da samarin Palasdinawa.
A cikin watannin bayan nan ana samun taho mu gama a tsakanin sojojin Sahayoniya da kuma samarin Palasdinawa da suke kokarin hana gina matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna a yammacin kogin Jordan.
Akwai dubban Palasdinawa a cikin gidajen Kurkukun ‘yan sayahoniya wadanda aka kama ba bisa wani kwakkwaran dalili ba.