IQNA

Martanin ‘yan Jarida Kan Gwamnatin Masar Dagane da Batun Alaka Da Isra’ila

23:40 - March 06, 2019
Lambar Labari: 3483430

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, a zaman da jami’an majalisun dokokin kasashen larabawa suka gudanar a birnin Aman na kasar Jordan a cikin wannan mako, wasu daga cikin kasashen larabawa sun bukaci a ci gaba da alaka da Isra’ila a tsakanin kasashen larabawa.

Kasashe uku ne kawai sukeda wannan ra’ayi wato UAE, Masar da kuma Saudiyya, amma dukkanin kasashen da suka halrci zaman taron ba su amince da haka ba.

A cikin bayanin bayan taron da aka rubuta kafin fitar da shi, an bayyana cewa dole ne dukkanin kasashen larabawasu dakatar da dukkanin wata mu’amala ko alaka da suke yi da Isra’ila a boye ko a bayyane, amma a nan take wakilan kasashen Saudiyya, Masar da UAE suka ce ba su amince dahakan ba, tare da jaddada goyon bayansu ga duk wani abin da zai kusantar da kasashen larabawaga Isra’ila.

Wannan matsaya da gwamnatin Masar ta dauka ta bakantawa al’ummar kasarta rai matuka, inda akasarin jaridun da suke fitowaa cikin wannan mako suke yin kakkausar suka ga gwamnatin kan wannan matsaya da ta dauka.

3795705

 

 

captcha