IQNA

22:19 - March 08, 2019
Lambar Labari: 3483435
Bangaren Kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana Saka Hizbullah a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda cewa gazawa ce daga makiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a lokacin da yake gabatar da wani jawabinsa a yammacin yau a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon dangane da tunawa da ranar kafa cibiyar karfafa gwagwarmayar al’ummar Lebanon, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana Saka Hizbullah a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda cewa gazawa ce daga makiya, domin kuwa Hizbullah ta yi musu yankan kauna ta hanyar hana su cimma burinsu a Lebanon da ma yankin.

Sayyid Nasrullah ya bayyana dukkanin matakan da ake dauka na sakawa kungiyar takunkumin karya tattalin arziki da cewa, yana a matsayin yaki ne a kan kungiyar.

Ya ce kamar yadda suka yi hakuri da tsayin daka da kuma fuskantar makiya a fagen yaki, haka za su hakuri da tsayin daka wajen fuskantar takunkuman da makiya suke kakaba musu.

Wannan bayani dais hi ne na farko da Sayyid Nasrullah ya gabatar tun bayan da Birtaniya ta saka kungiyar Hizbullah a cikin kungiyoyin ta’addanci a makon da ya gabata, lamarin da ya fuskanci kakausar suka daga gwamnatin Lebanon, kamar yadda kuma hatta kungiyar tarayyar turai ba ta amince da hakan ba, amma kasashen Amurka da Saudiyya da kuma Isra’ila sun yi lalae marhabin da hakan.

Dangane da kasar Lebanon kuwa, Sayyid Nasrullah ya ce kungiyar Hizbullah za ta ci gaba da ayyukanta kamar yadda ta saba, haka nan kuma dangane da yaki da cin hanci da rashawa kuma, kungiyar ta sha alwashin yin aiki kafada da kafada da gwamnatin Lebanon domin bankado masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa, inda ya ce kare kasar Lebanon bai takaita da yaki ba kawai, har ma da taimakawa a bangarori daban-daban domin ci gaban kasa da kuma al’umma.

3796181

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، taimakawa ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: