Kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, tun daa daren jiya kashe garin yau Laraba, sojojin Isra'ila suka fara yin dandazo , da shirin afkawa al'ummar Falastinawa mazauna yankin zirin Gaza biyo bayan hare-haren da Isra’ila ta kai yankin, da kuma harin mayar da martani da Falastinawa suka kai.
Wannan dai na zuwa ne bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Hamas da Isra'ila, inda Hamas take ci gaba da yin aiki da tsagaita wuta, yayin da Isra'ila kuma take ci gaba da yin shirye-shiryen yin wata tsokanar.
Rahotanni sun ce jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare har sau 30 a lokaci a cikin yankunan zirin Gaza a safiyar jiya Talata, inda rusa gidajen jama'a da kuma cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu.
Kimanin mako guda kenan da Isra'ila ta fara kaddaamr da hare-haren neman tsokana a kan Gaza, inda a nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa suka mayar da martani da makamai masu linzami har zuwa kusa da birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar gwamnatin yahudawan Isra'ila, tare da yin barna kan matsugunnan yahudawa.