Kamfanin dillancin labaran iqna, Jaridar Daily Mail ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, an samu mutanen ne da laifin bankawa takardun kur'ani wuta a wata makabarta da ke garin Qusur a kasar ta Pakistan, da nufin keta alfarmar littafin mai tsarki.
bayan da labarin haka ya watsu al'ummar yankin sun fitoa cikin fushi, inda suka fara lakadawa mutanen 7 duka, amma daga bisani jami'an tsaro sun kwace su, inda kuma kama su da laifin tozarta kur'ani mai tsarki.
Yanzu haka dai mutanen suna tsare, kuma ana sa ran kotu za ta yanke hukucni mai tsananin a kansua kan aikata wannan laifi.
Bisa dokokin kasar Pakistan tozarta wani abu daga cikin abubuwan girmama na addinin muslucni yana a matsayin baban laifi, wanda ake yanke hukucni mai tsanania kansa.