IQNA

Jagora: Riko Da Tafarkin Allah Shi Ne Dalilin Kiyayyar Amurka A Kan Iran

22:23 - April 04, 2019
Lambar Labari: 3483515
Jagoran juyin juyin halin musluncia kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana tsananin kiyayya da gaba da Amurka da wasu 'yan korenta irin Al Saud suke nuna wa Iran da cewa, sakamako ne na riko da tafarkin Allah da Iran din ta yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake gabar da jawabia  wurin taron tunawa da zagayowar ranar Mab'as, wato ranar da Allah ya aiko manzon Allah (SAW) da sakon manzonci wanda ya yi daidai da 27 ga watan Rajab.

Da farko dai jagoran ya fara mika sakon ta'aziyya da alhini ne ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa  ayankuna daban-daban na kasar a cikin 'yan kwanakin nan, inda ya yi fatan samun rahmar Allah ga dukkanin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hakan, da fatan samun lafiya ga dukkanin wadanda suka samu raunuka, haka nan kuma ya kirayi jami'an gwamnati da su ci gaba da kara kaimi wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu na taimaka ma dukkanin al'ummomin yankunan da abin ya shafa cikin gagawa, ba tare da samun tsaiko ba.

Jagora ya bayyana aiko manzon Allah (SAW) da Allah madaukakin sarki ya yi da cewa, wanann aike na musamman daga Allah madaukakin sarki ta hanyar wani mutum na musamman mai madaukakin matsayi na kololuwa a wurin Allah, shi ne ke bayyana matsayin sakon da kuma girmansa, domin kuwa sako ne na 'yantar da dan adam daga bautar duk wani abin halitta zuwa ga bautar mahalicci na gaskiya, kuma sako ne mai fitar da dan adam daga duhun jahilci zuwa ga hasken shiriya, sako ne da ke matsayin waraka ga dukkanin cutuka na ruhi ta hanyar kadaita ubngiji da mika wuya gare shi.

Ya ci gaba da cewa yin riko da farakin Allah da mika wuya zuwa ga umarnin Allah shi kadai yana tattare da abubuwa na jarabawa ga dan adam a kowane lokaci, daga ciki kuwa har fuskantar martani daga masu girman kai da ke dora kansua  matsayin masu kishinyar Allah wajen bautar da dan adam bisa bin manufofinsu.

Jagora ya ce, babban dalilin kiyayyar Amurka da wasu 'yan korenta irin Al saud a kan ita ce yin riko da tafarkin bin tafarkin Allah shi kadai, ba tare da mika wuya ga manufofin masu adawa da Allah da hankoron bauatr da dam ba, domin kuwa a cewarsa; dukkanin matsain lambar da Amurka da yahudawa suke yi kan kasar ta Iran, sakamko ne na kin mika wuya ga manufofinsu na zalunci da danniya  a kan al'ummomin duniya, wanda kuma wannan ita ce makomar duk wata al'umma da ta zabi ta rayu cikin 'yanci da karama, domin kuwa daga karshen lamari nasara da taimakon Allah yana tare ne da irin wannan al'umma.

Daga karshe jagoran ya jinjina wa dukkanin masu gwagwarmaya domin rayuwa a cikin daukaka da kuma samun 'yanci wajen bin sakon Allah da manzonsa ya zo da shi, ya ce dukkanin kungiyoyin gwagwarmaya a Palastine da Lebanon da Yemen da makamantansu, suna cikin sahu daya ne, wato sahun gwagwarmaya domin su rayu cikin karama da daukaka, da kuma 'yantuwa daga bautar masu girman kai na duniya, da kuma karnukan farautarsu masu aiwatar da manufofinsu a cikin al'ummar musulmi.

3800802

 

captcha