IQNA

22:30 - April 06, 2019
Lambar Labari: 3483524
A wani bayani da sojan kasar ta Libya suka fitar a yau Laraba, sun bayyana cewa; sun karbi umarni da su nufi yammacin kasar domin yakar ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna, bayanin ya kunshi cewa; Sojojin kasa za su nufi yammacin kasa zuwa biranen da suke yankin domin tsarkake su daga abin da ya saura na ‘yan ta’adda a cikin kasar Libya.

Shafin sojan kasar ta Libya ya wallafa wani bidiyo na rundunar Tariq Bin Ziyad, dake tafiya zuwa yammacin kasar.

Kasar Libya tana fama da rashin tsaro tun bayan kifar da gwamnatin Mu’ammar Khaddafi  da kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato ta yi.

An sami bullar kungiyoyi masu dauke da makamai a cikin kasar wadana suke da alaka da kungiyoyin al’ka’ida da kuma Da’esh.

To sai dai Mayakan gwmanatin hadin kan kasa sun ce sun yi nasarar korar sojojin Halifa haftar daga wani yanki mai muhimmanci a kusa da babban birnin kasar Tripoli.

Mayakan da su ka fito daga garin Zawiya sun kwace iko da wani shinge na soja mai nisan kilo mita ashirin da bakawai, daga birnin Tripoli bayan musayar wuta tsakaninsu da sojojin Halifa Haftar.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Janar Halifa Haftar ya bai wa sojojinsa umarnin su fara kai farmaki a yammacin kasar domin murkushe ‘yan ta’adda.

Mai Magana da yawun sojojin Libya da suke karkashin Halifa Haftar, Ahmad al-Mesmari ya bayyana cewa; Nan ba da jmawa ba za a bude wasu filayen dagar saboda sojoji sun tinkari birnin Tripoli ta kusurwowi da dama.

Kasashen duniya suna bayyana damuwarsu akan barkewar sabon rikici a cikin kasar ta Libya.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress ya ziyarci kasar ta Libya inda ya gana da dukkanin bangarorin da suke cikin rikicin. A jiya Juma’a ma Birtaniya ta yi kira yi taron gaggawa na Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya inda aka tattauna halin da kasar ta Libya take ciki.

3801056

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، gaggawa ، Haftar ، Libya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: