IQNA

0:20 - April 11, 2019
Lambar Labari: 3483539
Dakarun gwamnatin Libya mai mazauni a birnin Tripoli sun sanar da cewa, sun fatattaki dakarun Haftar daga babban filin sauka da tashin jiragen sama na Tripoli.

Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kakain rundunar sojin gwamnatin Libya mai mazaunia  Tripoli Muhammad Qanunu ya fadi jiya Talat a gaban manema labarai a birnin Tripoli cewa; sun kwace filin sauka da tashin jiragen sama na birnin, kuma yanzu yana karkashin ikonsu.

Ya ce a  halin yanzu babu wata matsala a cikin birnin Tripoli, domin komai yana tafiya yadda ya kamata bisa doka da oda, kuma suna ci gaba da kara fadada yankunan da suke hankoron shimfida ikonsu a yankunan da ke gefen birnin Tripoli.

Muhammad Qanunu ya kara da cewa, suna da cikakken shirin tunkarar dakarun Haftar, kuma za su fatattake su daga dukkanin wuraren da suka yada zangoa  kusa da birnin Tripoli.

3802400

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Libya ، Haftar ، Tripoli
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: