IQNA

21:59 - April 14, 2019
Lambar Labari: 3483544
Bangaren siyasa, masu halartar gasar kur’ani mai tsarkia  kasar Iran sun ziyarci jagoran juyin juya halin musulunci a gidansa da ke birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau masu halartar gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar Iran, sun gana da jagoran juyin juya halin musulunci, inda ya gabatar da jawabia  gare su.

A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa ya bayyana cewa, babbar hanyar da musulmi za su bi domin samun izza da wanzuwarta ita ce yin riko da koyarwar kur’ani mai tsarki a cikin dukkanin lamurransu.

Ya ci gaba da cewa, yin riko da koyarwar kur’ani an nufin komai ga musulmi, domin idan suka haka to za su zama masu hadin kai da kuma bin hakiakin koyarwar da manzon Allah ya yi wa musulmi kum aya dora su a kanta, idan kuma suka yi watsi da kur’ani, to kuwa tabbas sun yi watsi da hanyar koyarwa irin ta manzon Allah.

A yau aka shiga kwana na hudu na gasar kur’ani ta duniya da ake gudanarwa  a kasar Iran, tare da halartar baki daga kasashen duniya daban-daban, wanda ke gudana a babban masallacin marigayi Imam Khomenei (QS) da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.

3803478

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: