IQNA

22:55 - April 20, 2019
Lambar Labari: 3483562
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da tarukan nisf sha’aban a birnin Berlin na kasar jamus

Kamfanin dilalncin labaran iqna, za a gudanar da tarukan nisf shaaban a birnin berlin na kasar Jamus kamar yadda a aka saba a kowace shekara.

Majiyoyin cibiyar ahlul bait da ke birnin Berlin sun ce a yau an fara gudanar da dukkanin shiryeshiren da suka kamata domin gudanar da taron ranar sha biyar ga watan Sha'aban.

Daga cikin abubuwan da aka yi a yau har da raba abinci da abin sha ga mutane masu wucewa a gaban cibiyar musulmi da wadanda ba muuslmi ba, domin murnar zagayowar wannan rana mai albarka.

A gobe idan Allah ya kai mu za a gudanar da jawabai dangane da matsayin ranar, da jawabai kan Imam mahdi amincin Allah ya tabata a gare shi.

3805189

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Jamus ، Berlin ، tarukan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: