IQNA

Iran Da Pakistan Na Shirin kafa Runduna Ta Hadin Gwiwa

21:40 - April 22, 2019
Lambar Labari: 3483567
Kasashen Iran da Pakistan na shirin kafa wata runduna ta hadin gwiwa a tsakaninsu domin gudanar da ayyukan tsaroa kan iyakokinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, A lokacin da yake karbar bakuncin Firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan a yau a fadarsa da ke birnin Tehran, shugaban kasar Iran Hassan rauhani ya bayyana cewa, bangarorin biyu sun cimma matsaya kan kafa wata rundunar soji domin gudanar da ayyukan tsaro na hadin gwiwa  a tsakaninsu.

Shugaba Rauhani ya kara da cewa, kasashen Iran da Pakistan kasashe ne masu matukar muhimamnci a yankin, a kan haka tabbatar da tsaro a kan iyakokinsu na da matukar muhimmanci, musamman idan aka yi la'akari da barazanar ta'addanci da kasashen biyu suke fuskanta.

Shi ma a nasa bangaren Firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan ya bayyana jin dadinsa dangane da wannan matsaya da suka cimmawa tare da Iran, inda ya ce kasashen biyu za su ci gaba da yin aiki tare kafada da kafada a bangarorin tsaro, da sauran harkokin bunkasa tattalin arziki da ilimi da al'adu da sauransu.

3805590

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha