IQNA

23:19 - April 27, 2019
Lambar Labari: 3483582
Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad zarif ya ce siyasar Trump kan Iran ba za ta yi nasara ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad Zarif ya bayyana cewa, Amurka ba za ta iya cimma cimma burinta ta hanyar aiwatar da bakar siyasa a kan kasar Iran ba.

A lokacin da yake zantawa da tashar Fox News, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad Zarif ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka mai ci a yanzu tana aiwatar da siyasar wasu, duk kuwa da cewa hakan ya sabawa maslahar kasarta da al’ummarta.

A lokacin da aka tambayi Zarif kan cewa shin ko Saudiyya da UAE da kuma Isra’ila suna da nufin kifar da gwamnatin Iran ne? Zarif ya masa da cewa; kwarai kuwa babban burinsu kenan, kuma suna son su yi amfani da gwamnatin Trump wajen aiwatar da hakan.

Zarif ya kara da cewa ya san Trump yana yina bin yake yi ne domin maslahrsa ta jari hujja, ba domin maslahar Amurka da al’ummarta ba, amma duk da haka ba zai yi gigin shiga yaki da kasar Iran ba.

A cikin wannan makon ne sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompoe ya sanar da cewa; Amurka ba ta niyyar shiga yaki kai tsaye da kasar Iran.

 

 

3806649

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Trump ، Zarif ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: