IQNA

23:45 - May 01, 2019
Lambar Labari: 3483593
Bnagaren kasa dakasa, gwamnatin kasar Amurka ta saka kungiyar Ikhawan ta kasar Masar a cikin kungiyoyin da take kira na ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna, sakatariyar watsa labarai ta fadar mulkin Amurka Sarah Sanders ce ta bayyana cewa; Gamnatin Amurkan tana kan ganiyar shigar da sunan kungiyar “Ikhwanul-Muslimin” a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sanders ta kara da cewa; Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya tattauna da shugabannin hukumomin tsaro na kasar da kuma shugabannin yankin gabas ta tsakiya wadanda su ka bayyana masa tasu damuwar akan kungiyar ‘yan ‘uwa musulmi, don haka matakin yana tafiya daidai.

Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa; Trump ya ba da umarnin daukar matakin ne akan ‘Ikhwanul-Muslimin’ bayan ganawarsa da shugaban kasar Masar, Abdul Fattah al-Sisy.

Majiyar ta ci gaba da cewa; Daga cikin matakan da Amurka za ta dauka akan kungiyar ta “Ikhwanul-muslimin” da akwai kakaba takunkumi akan kamfanoninta da daidaikun mutanenta.

Gwamnatin Amurka dai tana yin amfani da makamin takunkumi a matsayin abin da zata cutar da duk wata kasa ko kungiya dabata bin manufofin siyasarta a duniya.

3807787

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: