Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jaridar Al-ahram ya abyar da rahoton cewa, ofishin shugaban kasar Masar ya fitar da sanarwar yin afuwa daga bangaren shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi ga mutane 89, wadanda aka saka su wakahi saboda basussuka.
A kowace shekara shugaba Sisi yana yin afuwa ga wani bangare na fursunonin da ake tsare das u a kasar ta Masar bisa dalilai daban-daban.
A cikin shekara ta 2014 ce Abdulfattah Sisi ya kafa wata kungiyar jin kai mai suna Tahya, wadda kan dauki nauyin biyan basussuka na mutanen da suka kasa biyan bashi har aka kai su wakahi.