IQNA

23:37 - May 10, 2019
Lambar Labari: 3483626
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani shfain kwafin kur’ani mai tsarki a baje kolin birnin Sharjah na hadaddiyar daular larabawa mai shekaru dubu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai ittihad ya habarta cewa, an nuna wani shfain kwafin kur’ani mai tsarki a baje kolin birnin Sharjah na hadaddiyar daular larabawa wanda aka rubuta sit un shekaru dubu da suka gabata.

Wannan shafin kur’ani an ajiye shi ne a garin Kirawan na kasar Tunisia, wanda daya ne daga birane da ka ajiye kayan tarihin musulunci.

Intesar Alubaidali babban daraktan baje kolin lttafai na birnin Sharjah ya bayyana cewa, wannan kur’ani an rubuta shit un karni na hudu hijira kamariyya.

Yace shafin yana dauk da rubtun ayoyin kur’ani mai tsarki aya ta 135 zuwa 137  cikin surat Nisa.

3810291

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: