IQNA

23:59 - May 11, 2019
Lambar Labari: 3483631
Bangaren kasa da kasa, fadar Vatican ta yi kira zuwa karfafa 'yan uwantaka tsakanin mabiyan addinain kiristanci da kuma musulucni a fadin duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani sakon da majalisar fadar Vatican ta PCID ta fitar  zuwa ga bangarori daban-daban na addinan kiristanci da musulunci, ta jaddada wajabcin ci gaba da kara karfafa kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin mabiya manyan addinai biyu na duniya, musulunci da kiristanci.

A cikin sakon vatican ta yi ishara bayyana wannan wata na Ramadan da cewa wata ne na ibada, wanda rahamar ubangiji take a  cikinsa, a kan haka lokaciun azumin Ramadan dama ta kara karfafa alaka tsakanin addinai.

Haka nan kuma wannan yana da tasiri a  cikin rayuwa ta zamantakewar jama'a, domin kuwa abubuwa da yawa suna hada al'ummomi mabiya addinai daban-daban, wanda kuma alaka ta 'yan adamtaka da girmama juna a  tsakaninsu, na taimakawa wajen samun zaman lafiya da fahimtar juna da kuma ci gabansua  dukkanin bangarori.

Daga karshe bayanin ya kirayi malamai da masana daga dukaknin bangarorin biyu da suka taka gagarumar rawa wajen ganin an samu damar cimma wannan buri na kara karfafa wannan alaka da kuma ci gabanta a tsakanin al'ummomi.

 

3810621

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، vatican ، musulunci ، kirista
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: