IQNA

Feqhizadeh ya ce:
13:38 - May 12, 2019
Lambar Labari: 3483632
An bude babban baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa karo na 27 a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, tare da gabatar da sabbin tsare-tsare a bangarori 126 da ake gudanar da baje kolin a kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Abdolhadi Feqhizadeh babban daraktan kasuwar baje kolin kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa ya bayyana cewa, an bode wannan baje koli nea  daren jiya Asabar, tare da halartar wakilai na dukaknin bangarori, da suka hada da cibiyoyin addini, da kuma ma’aikatun gwamnati, da wakilai daga majalisar dokoki, sai kuma malaman addini da masana daga jami’oi daban-daban.

Daga cikin bangarori 700 da aka gabatar ga babban kwamitin tantance ayyukan baje kolin, abubuwa 126 ne aka iya tantancewa wanda kuma  ahalin yanzu baje kolin zai takaita a kansu ne. daga ciki akwai nuna nau’oin kwafin kur’ani da aka rubuta su da kuma buga su ta hanyar yin amfani da fasaha ta musamman ta zamani, sai kuma wasu sauran bangarorin ad suka shafi yadda aka samar da hanyoyi rubutun kur’ani ta yanar gizo da kuma hada sautukan karau domin koyarwar cikin sauki, sauran bangarori wadanda a karon farko ne aka fara nuna su.

Haka nan kuma taron baje kolin wanda shi ne karo na ashirin da bakwai da ake gudanar da shia  cikin wane watan aumin ramadan mai alfarma, yana samun halartar wakilan kamfanonin buga littafai na cikin cikin gida kuma na kasashen ketare, inda kamfanoni daga kashe 10 na musulmi suka kawo nasu kayan da suke samarwa a bangaren ayyukan kur’ani.

3810641

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kayan ، kamfanonin ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: