IQNA

23:53 - May 13, 2019
Lambar Labari: 3483635
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Abbas Musawyi ya ce, Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta nuna damuwa akan farmakin da gangan da aka kaiwa ga wasu jiragen ruwa a tashar ruwan Fujaïra.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Abbas Moussavi, ya ce yana da kyau a gudanar da bincike kan ire iren wadannan al’amuran dake faruwa, saboda hakan babbar barazana ce ga sha’anin tsaro da kuma zurga zurga ta jiragen ruwa a yankin Golf.

Iran dai na mai danganta lamarin da yadda wasu kasashe ke kokarin wargaza tsaron kan ruwa.

A jiya ne dai hadaddiyar daular larabawa, ta tabbatar da cewa an kai wasu ayyuka data danganta dana aika-aika kan wasu jiragen ruwa na ‘yan kasuwa a gabashin Fujairah, saidai ba tare da bayyana wadanda suka aikata hakan ba.

3811053

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: