IQNA

21:15 - May 22, 2019
Lambar Labari: 3483665
Wasu gungun yahudawa masana da kuma masu bincike sun nuan goyon bayansu ga kungiyoyin da ke yin kira da a haramta kayan Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a zaman da majalisar dokokin kasar Jamus ta gudanar a karshen mako, ta tattauna kan daftarin kudirin da aka gabatar mata, da ke neman a haramta kungiyoyin da ke yin kamfe na kiran jama’a domin su daina sayen kayan da Isra’ila take samarwa.

A daya bangaren kuma wasu daga cikin yahudawan kasar ta Jamus masu adawa da siyasar Isra’ila, sun fito sun nuna cikakken goyon bayansu ga kungiyoyin da ke yin kira da a kauracewa sayen kayan Isra’ila a kasar.

Matakin wadannan masana yahudawa bai tsaya ga goyon bayan haramta kayayyakin da Isra’ila take samarwa ba kawai, har ma sun fitar da doguwar wasika da ke kiran majalisar dokokin kasar ta Jamus da ta yi watsi da daftarin kudirin da ke kira da a haramta kungiyoyi masu kira da a kauracewa kayan Isra’ila, inda jama’a suke sanya hannu a kan takardar.

Akwai kungiyoyin yahudawa da dama a cikin kasashen turai da suke adawa da siyasar Isra’ila ta zalunbci da danniya da kisan kiyashi a kan al’ummar palastine, inda suke ganin hakan ya sabawa koyarwar addinin yahudanci.

3813797

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، yahudawa ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: