IQNA

Karim Mansuri ya Gabatar Da Karatun Kur’ani A Ghana

23:57 - May 23, 2019
Lambar Labari: 3483667
Bangaren kasa da kasa, Karim Mansuri fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki ya gabatar da karatu a Husainiyar mutanen Lebanon a kasar Ghana.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Karim Mansuri makarancin kur’ani mai tsarki dan kasar Iran ya gabatar da karatu a kasar Ghana kasar da tun kwanaki 10 yake ziyartarta.

Ya gabatar da karatu a wurare daban-daban na kasar tare da halartar musulmi a cikin wanann wata na Ramadan.

A jiya ma gabatar da karatun kur’ani mai tsarki Husainiyar mutanen Lebanon da ke birnin Accra fadar mulkin kasar, inda ya karanta ayoyi na 4 da 5 a cikin surat Yusuf ayoyin da ke cewa ( A lokacin da Yusuf ya ce ya babana ni na yi mafarki naga taurari goma sha daya da rana da wata na gan su suna yi mani sujada) ( yace kada ka bayyana mafarkinka ga ‘yan uwanka sai shirya maka makirci, hakika shi shaidan makiyin mutum ne mabayyani).

Za a iya duba faidan bidiyon tilawar a nan:

3814157

 

 

captcha