IQNA

23:57 - May 24, 2019
Lambar Labari: 3483669
Bangaren kasa da kasa, hukumar Hizba mau kula da hakokin addini a jihar Kano ta kafa dokar hana cin a bainar jama'a a cikin fadin jihar Kano.

Kamfanin dillancin labara iqna, Adamu Yahya kakakin hukuma Hizba mai kula da hakokin addini a jihar Kano ya  bayyana cewa hukumat ta kafa dokar hana cin a bainar jama'a a cikin fadin jihar Kano domin kiyaye alfarmar wannan wata.

Ya ci gaba da cewa bisa shari'a ta addini ana girmama watan ramadan mai alfarma, daga cikin hanyoyin girmama wanann wata har da kaure ma cin abinci a bainar jama'a, ko da mutum baya yin azumi saboda wata larura.

Haka nan kuam ya yi ishara da cewa, wanann doka tana shafar musulmi kawai wadanda suka yi imani da kuma yarda da azumi cewa uamrnin Allah ne.

Tuna  shekara ta 2000 ce aka kafa wannan wannan kungiya wadda ta ke sanya ido a kan kiyaye kaidoji da dokoki na addinin musulucni a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Kamar yadda kuma hukumar takan gudanar da ayyuka da suka shafi daidaita lamurra na zamantakewar musulmi, kama daga yin sulhu da kuma raba husuma da dai sauransu.

 

3814189

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، najeriya ، azumi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: