IQNA

'Yan Huthi Sun Kai Hari Kan Yankin Jizan Na Saudiyya

0:00 - May 27, 2019
1
Lambar Labari: 3483677
Kungiyar Ansarullah ta kaddamar da hare-hare da jiragen yaki marassa matuki a kan filin sauka da tashin jiragen yakin Saudiyya da ke Jizan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto cewa, tashar Almasirah ta kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, dakarun Ansarullah sun harba makamai masu linzami ta hanyar jirage marassa matuki a kan filin sauka da tashin jiragen yakin saudiyya a Jizan da ke kusa da iyaka da kasar Yemen.

Rahoton ya ce hare-haren na zuwa a wani mataki na daukar fansa kan kisan mata da kanan yara da rusa masallatai da makarantu da cibiyoyin ilimi da na kiwon lafiya da Saudiyya da ‘yan korenta suke yi a kasar Yemen ne, inda a cikin wannan makon hare-haren saudiyya sun yi sanadiyyar mutuwar mata da kananan yara a yankuna daban-daban a cikin gundumomin Hajja, Ta’iz da kuma San’a.

A cikin makon da ya gabata ba mayakan na Ansarullah sun harba makamai masu linzamiakan daya daga cikin manyan matatun mai na kasar Saudiyya harin da ya yi babbar barna, duk kuwa da cewa daga bisani mahukuntan na Saudiyya sun da’awar cewa an harba makaman kan biranan Makka da Jiddah ne, ba tare da nuna wata hujja ko alama da za ta iya tabbatar da hakan ba.

3814737

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Hakan yayi dai dai suma suji yadda yan yamen din keji
captcha