IQNA

Jam’iyyar Wifaq Ta Fitar Bayani kan Zaman Makka

14:50 - May 30, 2019
Lambar Labari: 3483687
Jam’iyyar Alwifaq ta kasar Bahrain ta fitar da bayani kan zaman shugabannin larabawa a Makka.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, shafin yada labarai na Almanar ya bayar da rahoton cewa, jam’iyyar Alwifaq ta kasar Bahrain wadda ita ce jam’iyyar siyasa mafi girma a kasar, ta kirayi mahalrta taron na Makka da su tatatuna abin da zai zama alhairi ga yankin.

A cikin bayanin da ta fitar a daren jiya, jam’iyar ta Alwifaq ta bayyana cewa, akwi matsaloli masu tarin yawa da ake fama da su a yankin gabas ta tsakiya da suke ci ma al’ummomin yankin tuwo a kwarya, wadanda ya kamata taron ya mayar da hankali a kansu.

Bayanin ya kara da cewa, idan masu taron suka dauki kwakkwarar matsaya kan matsalolin yankin gabas ta tsakiya da kuma yadda za a warware su ta hanyar fahimtar juna a tsakanin dukaknin kasashen yankin, to wannan shi ne abin da zai kawo zaman lafiya a yankin, amma yin wani abu sabanin haka, to zai kara dagula lamurra ne kawai.

Babbar manufar wannan taro dai kamar yadda masu masaukin bakin suka sanar shi ne, tatatuna batun harin Fujaira, wanda tuni suka dora alhakin hakan a kan Iran bayan da Amurka ta furta hakan, ba tare da gabatar da wani dalili ba.

3815698

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha