IQNA

Taro Kasashen Musulmi Ya Mayar Da Hankali Kan Palestine

23:53 - June 01, 2019
Lambar Labari: 3483699
Bangaren kasa da kasa, taron kasashen musulmi ya mayar da hankali kan batun Palestine da kuma wajabcin taimaka ma Falastinawa domin kafa kasarsu mai gishin kanta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bayanin bayan taron na shugabannin kasashe mambobi a kungiyar OIC, ya mayar da hankali kan halin al’ummar Palestine suke ciki, da kuma abin da ya rataya kan dukkanin kasashe na taimaka musu.

Haka nan kuma bayanin ya nuna rashina mincewa da mayar da ofishin jakadancin Amurka a birnin Quds, tare da amincewa da birnin a matsayin babban birnin Isra’ila.

Kamar yadda bayanin kuma ya tabo batun halin da musulmin kabilar Rohingyasuke a kasar Myanmar, tare da yin Allawadai da kisan gillar da sojojin kasar gami da a’yan addinin buda suka yi a kansu.

Haka nan kuma bayanin ya tabo yadda kyamar musulmi ke karuwa a cikin wasu kasashe musamman kasashen nahiyar turai, da yadda ake cutar da su, tare da jaddada wajabcin kare hakkokin musulmi a duk inda suke.

An kafa kungiyar ne a shekara ta 1969, wadda ta hada kasashen musulmi da kuma wasu kasashe a matsayin masu sanya ido.

3816208

 

captcha