IQNA

Sarkin Muslmi A Najeriya Ya Yi Kira Da Su Fara Dubar Wata

23:02 - June 03, 2019
Lambar Labari: 3483703
Sarkin musulmi Alh. Muhammadu sa’adu Abubabakr ya kirayi al’ummar msuulmi a Najeriya das u fara dubar watan shawwal daga yammacin yau Litinin.

Kamfanoin dillanicn labaan iqna, a cikin bayanin da sarkin ya fitar, sarki Muhammadu sa’adu Abubabakr bayan yin addu’a ga dukaknin musulmi a kan Allah ya karbi ibadarsu a cikin wannan wata mai alfarma, ya kuma bukaci da a duba watan Shawwalayau a rana ta 29 ga watan Ramadan mai alfarma.

Sarki ya ce idan aka samu wasu yankuna an ga wata tare da amintattun shedu, toza a sanar da gobeamatsayin ranar farko ta watan Shawwal, wato ranar idin karamar salla.

Kamr yadda kuma ya umarci majalisar malaman kasar da ta sanya ido kan batun ganin watan, domin tabbatar da ingancin ganinsa ko akasin hakan.

A bisa al’ada dai sarkin musulmi ne ke bayar da umarnin ganin wata a lokacin azumi domin musulmi a Najeriya su tashi da azumi, kamar yadda kuma shi ne ke bayar da sanarwar ganin watan Shawwal domin ajiye azumi a fadin kasar.

3817043

http://iqna.ir/fa/news/3817043

captcha