IQNA

23:46 - June 04, 2019
Lambar Labari: 3483708
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taro a birnin London mai taken mahangar Imam Khomeini (RA) kan matsayin hankali a rayuwar mutum.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a yau an gudanar da taro a birnin London na kasar Birtaniya, mai taken mahangar Imam Khomeini kan matsayin hankali da adalci a rayuwar mutum.

A kowace shekara na gudanar da irin wannan zaman taro a ginin babbar cibiyar muulunci da ke birnin London tare da halartar malamai da masana.

Sayyid Abbas Naghavi shi ne ya fara gabatar da jawabi a wurin taron, inda ya tabo wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar marigayi Imam khomeni da kuma darussan da suke cikin rayuwar tasa.

Haka nan kuma wasu daga cikin 'yan siyasa da suka halarci wurin sun tofa albarkacin bakinsu dangane da rayuwar Imam Khomenei.

Sayyid Qasim Jalali daya daga cikin malamai masu kula da cibiyar muslunci a birnin London ya gabatar da nasa jawabin wanda shi ma ya tabo bangaren rayuwar gwagwarmaya da nemen 'yancin al'ummomi da Imam ya shara da shi.

 

3817175

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، London ، taro ، imam khomeni
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: