IQNA

23:51 - June 06, 2019
Lambar Labari: 3483714
Bangaren kasa da kasa, an fara rijistar sunayen wadana suke da sha'awar shiga gasar kur'ni ta kasa baki daya a Masar.

Kamfanin dillancin labara iqna, an fara gudanar da rijistar sunayen masu shirin shiga gasar kur’ani ta kasar Masar ta wannan shekara.

Ma’ikatar kila da harkokin addini ta kasar Masar ce ta bayar da sanarwar, kuma tuni aka riga aka fara yin rijista wadda za ta ci gaba har zuwa karshen wannan wata na Yuni da muke ciki.

Bayanin ya kara da cewa, an sanya sharudda ga duakkanin wadanda suke da bukatar shiga gasar, da kuma suka hada cewa dole ne mutum ya zama yay i karatu a wani reshi na jami’ar Azhar.

Baya ga haka kuma an kasa bangarorin gasar zuwa kashi uku, kashi na farko wanda zai hada da harda da kuma tajwdi gami da tilawa, wanda kuma dole ne wanda zai shiga wanna bangaren shekarunsa kada su wuce 35.

Sai kuma bangare na biyu shi ne ya hada da harda da kuma tajwidi, wanda shi ma mai shiga wannan bangaren kada shekarunsa su wuce 30, kamar yadda bangae na karshe shi ne bangaren harda, wanda shi ma ‘yan kasa da shekaru 25 ne za su gudanar da shi.

 

 

 

 

3817382

 

http://iqna.ir/fa/news/3817382

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: