IQNA

23:59 - June 11, 2019
Lambar Labari: 3483730
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron Isra'ila sun kame wani kusa a kungiyar gwagwarmayar falastinawa ta Hamas.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne jami’an tsaron gwamnatin yahudawan suka kai samame a  gidan Ra’fat Nasif, daya daga cikin manyan jagorin kungiyar Hamas, a garin Tulkaram da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Rahoton ya ce jami’an tasron gwamnatin yahudawan sun tafi da Ra’fat wani wuri da ba a sani ba.

Tun kafin wannan lokacin dai Isra’ila ta sha kama Ra’afat tana tsare a gidan kaso, inda ya kwashe kimanin jimillar shekaru 18 a gidan kason Isra’ila, kamar yadda a halin yanzu ma suka sake kame shi ba tare da tuhumarsa da aikata wani laifi ba.

 

3818517

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، palastine ، Hamas
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: